9 Afirilu 2016 - 17:28
Zarif: Iran Da Rasha Za Su Ci Gaba Da Aiki Tare A Dukkanin Bangarori

Zarif Iran Da Rasha Za Su Ci Gaba Da Aiki Tare A Dukkanin Bangarori

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, kasashen Iran da Rasha za su ci ga da yin aiki kafada da kafada a dukkanin bangarori.

Zarif ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Itar-fas a birnin Baku na kasar Azarbaijan, inda ya ce; Iran da Rasha za su ci gaba da yin aiki tare a bangarori daban-daban, da hakan ya hada da batutuwa na tattalin arziki da cinikkaya, da kuma batutuwa da suka shafi tsaro da ayyukan soji.

 Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa, ta fuskar tsaro kasashen biyu sun taka rawar gani tare da gwamnatin Syria wajen karya lagon manyan kungiyoyin 'yan ta'adda na ISIS da Nusra, wadanda Isra'ila tare da wasu kasashen larabawa suke daukar nauyinsu, ya kara da cewa Rasha da Iran ba su taba amincewa da kokarin da wasu ke yi na haifar da rikici da sunan addini a yankin gabas ta tsakiya ba.288